Farfado da hulda tsakanin Jamus da Turkiyya | Labarai | DW | 06.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farfado da hulda tsakanin Jamus da Turkiyya

Ministocin harkokin waje na Jamus da Turkiyya za su gana kusa da birnin Berlin, da nufin sake farfado da hulda tsakanin kasashen biyu bayan da ta yi tsami a tsahon kusan shekara guda.

Mevlüt Gavusoglu na Turkiyya da Sigmar Gabriel na Jamus za su hadu a Goslar da ke da nisan kilomita 250 daga birnin Berlin. Dangantaka tsakanin Jsamus da Turkiyya ta yi tsami tun lokacin wani yunkurin juyin mulkin da sojoji suka yi a Turkiyya wanda ya ci tura, kana daga baya gwamnatin Turkiyya ta kame mutane sama da dubu 20. Tun farko gwamnatin Jamus ta gargadi 'yan yawan shakatawa na kasarta da su  kauce wa zuwa Turkiyya, da kuma haramta wa kamfanonin Jamus saka jari a Turkiyyar sakamakon yadda a baya-baya nan hukumomin Turkiyyan ke tsare  da Jamusawa da dama a gidan kurku.