Farautar maharan birnin Paris | Labarai | DW | 18.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farautar maharan birnin Paris

Jami'an tsaro a Faransa na ci gaba da farautar wadanda ake zargi da kitsa harin da aka kai a birnin Paris a karshen makon da ya gabata.

Farautar maharan Faransa

Farautar maharan Faransa

Rahotannin sun nunar da cewa an ji harbe-harbe a yankin Saint Denis da ke arewacin birnin Paris da sanyin safiyar wannan Laraba, wanda aka hakikance yana da nasaba da harin na makon jiya. Tashar talabijin ta RTL ta ruwaito wani shaidan gani da ido na cewa ya ji kara mai karfi kafin daga bisani ya ji karar musayar harbe-harbe da bindigogi na tsahon mintuna 10. Kawo yanzu dai an tabbatar da cewa mutane uku cikin wadanda ke gidan da jami'an tsaron suka yi wa kawanya sun mutu ciki kuwa har da wata mace da ta tarwatsa kanta da abubuwa masu fashewa, kana sun cafke mutane uku. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito wani na kusa da jami'an tsaron da ya nemi a sakaya sunansa na cewa jami'an 'yan sanda da dama sun jikkata a yayin musayen harbe-harben na Saint Denis, ko da yake 'yan sanda sun bayyana cewa hudu daga cikin jami'ansu sun samu raunuka a kokarin da suke na farautar daya daga cikin wadanda ake zargi da kitsa harin na Paris Abdelhamid Abaaoud da kuma wasu da ake zargin yana tare da su. Kawo yanzu dai 'yan sandan sun tabbatar da cewa akwai sauran mutum guda a cikin gidan da suka yi wa kawanyar.