1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farautar Joseph Kony da ƙungiyar tawayensa ta LRA

April 7, 2013

Dakarun Uganda sun sha alwashin zaƙulo jagorar ƙungiyar 'yan tawayen LRA Joseph Kony to ta halin ƙaƙa, kuma sun ci sauyin mulki a Bangui ba zai shafe su ba

https://p.dw.com/p/18BLg
(FILES) A file photo taken on November 12, 2006, shows the leader of the Lord's Resistance Army (LRA), Joseph Kony, answering journalists' questions in Ri-Kwamba, southern Sudan, following a meeting with UN humanitarian chief Jan Egeland. Uganda's rebel Lord's Resistance Army vowed on September 13, 2008 to sign a final peace deal but warned it will not disarm until International Criminal Court arrest warrants for alleged war crimes are 'resolved'. LRA spokesman David Nyekorach-Matsanga said rebel chief Joseph Kony was willing to sign the much delayed peace deal, speaking as military pressure mounts against the northern Ugandan insurgents. AFP PHOTO /STUART PRICE (Photo credit should read STUART PRICE/AFP/Getty Images)
Joseph KonyHoto: Stuart Price/AFP/Getty Images

Dakarun sojin Uganda sunce zasu cigaba da farautar 'ya'yan ƙungiyar tawayen nan ta Lord's Resistance Army ko kuma LRA, a Jamhoriyar Afirka Ta Tsakiya duk da zargin da aka yi na cewa ta daina gudanar da ayyukanta a yankin.

Haka nan kuma sauyin gwamnati a Bangui ba shi da wani tasiri kan ƙudurin hukumomin Ugandan na neman zaƙulo jagorar ƙungiyar wato Joseph Kony, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, lokacin da take maimaita kalaman Francisco Madeira, manzon ƙungiyar Tarayyar Afirka kan wannan batu.

Manzo na musamman na Jamhoriyar Afirka Ta Tsakiya a Majalisar Dinkin Duniya Abou Moussa shi ma ya bada tabbacin cewa ƙasarsa zata yi iya ƙoƙarinta wajen ganin an gano Joseph Kony.

Rahotanni na nunar da cewa Joseph Kony na ɓuya ne a yankin da ke kusa da iyakar ƙasashen Jamhoriyar Afirka Ta Tsakiya, Sudan da Kudancin Sudan.

Kony da ƙungiyarsa da ta yi ƙaurin suna saboda amfani da ƙananan yara a aikin soji, da yanka gaɓoɓin waɗanda suka kama da ma fyaɗe da cin zarafin mata, ta yi shekaru 25 yanzu tana bijire wa gwamnatin Uganda.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal