Farashin barema ya yi tsada a Nijar | Zamantakewa | DW | 01.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Farashin barema ya yi tsada a Nijar

Masu gonaki a jamhuriyar Nijar na fuskantar babbar kalubale na tsadar farashin masu aikin noma wato 'yan barewama ko 'yan mantaka. Wannan kuwa na zuwa ne a yayinda daminar bana ta sauka gadan-gadan domin fara aikin gona.

Masu aikin gona

Masu aikin gona

Majiya karfi da ke aikin noman kudin na ci gaba da kara farashin aikin su ne a kan dalilin wahalar da aikin ke tattare da su, ko da yake dai farashin aikin na barema ya danganta daga yanki zuwa yanki da kuma yanayi.

Burundi Landwirtschaft (picture alliance/africamediaonline)

Wasu mata na aikin noma a gona

 

Wasu masu aikin na Mantaka na alakanta kara farashin ne bisa la'akari da abinda za su ci da kuma sauran abubuwan yau da kullum na more rayuwa. A jihohi kamar Konni masu aikin na karbar jaka uku. A yanzu dai wannan dalili na rashin biyan kudin aikin noman, masu bareman na cewa sun fi karbar aikin kwantiragi inda mutane 40 ke wa aikin gona mai girman Eka 10 taron dangin su nome shi cikin kwanaki bakwa a kan farashin jaka 110 kacal wato naira 600 kenan a darajar kudin na NIjar a yanzu.  Ana dai alakanta tsadar aikin baremar ne da yadda matasan kasar Nijar ke kauracewa aikin noma a wannan zamani.

Mosambik Landwirtschaft (dapd)

Mai gona na duba amfanin gonarsa

To sai dai wasu sun fi gane amfani da motocin noma irin na zamani ko dabbobi da ake daurawa galman noma, masu kananan karfi na ganin masu aikin na Mantaka na tsaulawa wanda suke ganin ka iya haifar da kalubale ga harkokin noma na bana.