Farar hula cikin wahala a Yemen | Labarai | DW | 06.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farar hula cikin wahala a Yemen

Kungiyar agaji ta Red Cross ta bukaci da a kara daukar tsauraran matakai domin ba da damar ganin farar hula sun samu agaji gagawa.

Sakamakon mummunar yaki da ake gwabazawa a Yemen wanda hakan ya kan janyo tarnaki ga ayyukan jin kai, ya janyo karancin abinci da ruwan sha da kuma rashin magunguna. Barin wutar da ake yi tun ranar juma'a  a birnin Sanaa ya sa jama'a sun makale a gidajensu, yayin da kuma rokokin da ake harbawa a birnin suka lalata wani rumbun ajiye magungunan na kungiyar agaji ta Red Cross wadanda take shrin rarrabawa a cikin wasu  asibitoci guda uku wadanda ke fama da karancin magunguna da kuma rashin wutar lantarki.