Faransa za ta yi wa tsarin mulkinta kwaskwarima don maganin ′yan tarzoma | Labarai | DW | 23.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa za ta yi wa tsarin mulkinta kwaskwarima don maganin 'yan tarzoma

Bayan hare-haren da aka kai birnin Paris ciki watan Nuwamba shugaba Francois Hollande ya ba da sanarwar yi wa kundin tsarin mulkin gyara.

Gwamnatin Faransa za ta shigar da dokar ta-baci cikin kundin tsarin mulkin kasar. Firaminista Manuel Valls ya sanar a birnin Paris cewa majalisar ministoci ta amince da yi wa tsarin mulkin gyaran fuska. Kafin wannan canjin ya zama doka dole sai majalisar wakilai da ta dattawa sun amince da shi da rinjayen kashi uku bisa biyar na wakilan majalisun guda biyu. Firaminista Valls ya ce a ranar 3 ga watan Fabrairu za a fara muhawara a majalisa kan yi wa kundin tsarin mulkin wannan kwaskwarima. Jim kadan bayan hare-haren nan na birnin Paria a ranar 13 ga watan Nuwamba shugaban Faransa Francois Hollande ya ba da sanarwar yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima. Kawo yanzu wata dokar kasar ce ta tanadi kafa dokar ta-baci a kasar.