Faransa za ta mika Ngaissona ga kotun ICC | Labarai | DW | 31.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa za ta mika Ngaissona ga kotun ICC

Hukumomi a Faransa na shirin mika wani tsohon madugu a kungiyar Anti-Balaka ta Jamhuriyar Afirka ta tsakiya Patrice-Edouard Ngaissona domin fuskantar shari'a a kotun duniya ta ICC da ke Hague.

Wata kotu a Faransa a yau Litinin ta yanke hukuncin mika Patrice-Edouard Ngaissona daga gidan yarin da ake tsare da shi a kusa da Paris zuwa kotun kasa da kasa da ke Hague, inda zai fuskanci shari'a kan laifukan yaki da ake zarginsa da hannu, a matsayin babban kwamanda na kungiyar 'yan tawayen Anti-Balaka a Jamhuriyar tsakiyar Afirka.

Ngaissona wanda tsohon minista ne a gwamnati, a watan Fabrairu aka zabe shi a kwamitin koli na hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF duk da cewa kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya Human Wrights Watch ta ayyana shi a cikin shugabannin kungiyar Anti-Balaka a rahoton da ta fitar a shekarar 2016.

Kungiyar ta Kiristoci ta aiwatar da kisan mummuke akan musulmi a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya tsakanin shekarar 2013 zuwa 2014 yayin wani rikicin kabilanci da na addini da ya karade kasar, bayan kungiyar musulmi ta Seleka ta hambarar da gwamnatin Francois Bozize a 2013.