Faransa za ta bai wa Ƙurdawan Iraƙi makamai | Labarai | DW | 13.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa za ta bai wa Ƙurdawan Iraƙi makamai

Faransa ta ce za ta aike da makamai a cikin sao'i masu zuwa domin ƙarfafa gwiwa ga dakarun gwamnati da na mayaƙan Ƙurdawa.

A cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin ƙasar ta bayyana ta ce ta yi haka ne bisa buƙatar hukumomin Iraƙin sakamakon yadda mayaƙan ISIS ke ƙara tinkarar birnin Bagadaza tare da kashe fararan hula.

Tun farko Amirka ta yi gargaɗin za ta yi nazarin kwashe wasu farar hula tsiraru 'yan ƙabilar Yazidis wanda suka sarƙe a cikin tsaunika a arewacin Iraƙin. Wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yawansu ya kai dubu 30 waɗanda kuma ta ce suna fuskantar barazanar kisan kare dangi daga masu kishin addinin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu