1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta amshi 'yan gudun hijira 800

Zulaiha Abubakar
June 16, 2018

Gwamnatin Spain ta sanar da amincewarta kan kiran da kasar Faransa ta yi mata na karbar 'yan gudun hijirar Afirka da ke watangariri a teku tun cikin makon daya gabata.

https://p.dw.com/p/2zhCb
Italien Flüchtlinge auf dem Schiff Aquarius
Hoto: picture-alliance/dpa/Kenny Karpov/SOS Mediterranee

Ana sa ran jirgin ruwa mallakar kasar Faransa da ya ceto 'yan gudun hijirar fiye da dari shida wadanda suka haddasa cece-kuce tsakanin kasashen d ake kungiyar Tarayyar Turai  zai isa spain a gobe Lahadi kamar yadda mataimakin Firaminisatan kasar Carmen Calvo ya sanar. Ya kuma kara da cewar kasar Faransa ta dauki alwashin yin aiki tare da Spain don nemar wa 'yan gudun hijirar mafita,

Mafiya yawan 'yan gudun hijirar wadanda suka hada da maza magidanta dari hudu da hamsin da mata tamanin ciki kuwa har da masu tsohon ciki da yara kanana goma sha daya da kuma samari da 'yan mata da adadinsu ya kai 93 sun fito ne daga kasashen Afirka da Bangaladesh da kuma Pakistan .

Tun da fari dai gwamnatin kasar Italiya mai kyamar baki ce ta ki amincewa da Jirgin ceton ya sauke tulin 'yan gudun hijirar kafin kasar Spain tace taji ta gani. 'Yan Afrika na sahun gaba wajen kwarara kasashen Turai don samun waraka daga matsin tattalin arziki a kasashen su.