1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta soki shirin kakaba wa wasu kasashe takunkumi

Ramatu Garba Baba MNA
July 26, 2017

Faransa ta ce takunkumin da Amirka ta shirya kakaba wa kasashen Rasha da Koriya ta Arewa da kuma Iran sam bai dace ba domin kuwa ya sab awa dokokin kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/2hBnU
USA Wahl zur Aufhebung von Obamacare
Hoto: Reuters

Faransa ta ce sabbin takunkuman da Amirka ta shirya kakabawa kasashen Rasha da Koriya ta Arewa da kuma Iran sam bai dace ba domin kuwa ya saba wa yarjejeniya karkashin dokokin kasashen duniya, Wannan dai ya biyo bayan kuri'ar da majalisar wakilan Amirka ta kada a ranar Talata, inda ta amince da a sanya wa wadannan kasashen takunkuman. Ana ganin wannan matakin zai iya shafar tattalin arzikin kasashen yankin Turai, abin da ya sa ma'aikatar harkokin wajen Faransa da ta fitar da sanarwar a wannan Laraba ta ce akwai bukatar aiwatar da wasu sauyi a dokokin kungiyar EU da kuma shirya zama don tattauna batun.

Tuni dai kasar Rasha ta bakin ministan harkokin cikin Sergei Lavrov, ta mayar da martani inda ta gargadi Amirka kan daukar wannan matakin. Ana shi bangaren shugaban kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya bayyana bacin ransa, inda ya kuma ce za su dauki matakin da ya dace nan bada jimawa ba. Ya kuma kara da cewa takunkumin da Amirka ke son aza wa kasashen zai iya yin illa ga tattalin arzikin nahiyarsu.