1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe shugaban IS na Sahel

September 16, 2021

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce dakarun Faransa sun kashe shugaban kungiyar IS a yankin Sahara Adnan Abu Walid al-Sahrawi.

https://p.dw.com/p/40NnJ
Abu Walid I Adnan Abu Walid al-Sahrawi
Hoto: The U.S. Department of State/Wikipedia

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter da safiyar yau Alhamis (16.9.2021), shugaba Macron ya ce hakan wani ci gaba ne da aka samu a yakin da ake yi da ta'addanci a yankin Sahel.

Kungiyar ta ISGS na zafafa kai hare-harenta a yankin Sahel, musamman ma a iyakar kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso kana kungiyar ta dauki alhakin kai harin da ya kashe wasu sojojin Amirka a shekarar 2017 da kuma kisan ma'aikata shida na wata kungiyar mai zaman kanta ta Faransa a watan Augustan bara.