Faransa ta sake jaddada muhimmancin China a batun sauyin yanayi | Labarai | DW | 02.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta sake jaddada muhimmancin China a batun sauyin yanayi

Shugaba Francois Holland ya bayyana tallafin na China da cewa gagarumi ne kasancewar batun na sauyin yanayi abu ne da ya shafi baki dayan al'ummar duniya.

Frankreich China Präsident Xi Jinping bei Francois Hollande in Paris

Shugaba Xi Jinping da Francois Hollande

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande a ranar Litinin din nan ya bayyana cewa tallafin da kasar China za ta bayar kan batun cimma matsaya a taron koli da za a yi nan gaba a birnin Paris, abu ne da ke zama mai muhimmancin gaske. Shugaba Holland ya bayyana haka ne a ziyarar da ya fara a wannan kasa da ke zama babba a nahiyar Asiya.

Da yake jawabi a birni na Chongqing da ke a kudu maso yammacin China ya ce yana cike da fata na ganin shugabannin kasashen duniya sun ba da hadin kai da ya dace ta yadda za a rage dimamar yanayi ya zuwa digiri biyu a ma'aunin zafi. Ya ce tallafin na China gagarumi ne kasancewar batun na sauyin yanayi abu ne da ya shafi baki dayan al'ummar duniya, ta yadda za a yi tattalin muhallin dan Adam, kuma batu ne da ke da muhimmanci ga tattalin arzikin kasashen a fafutikar da ake ta ganin an samar da ci-gaba ba tare da gurbata muhalli ba ta hanyar abin da ake kira green growth a Turance.

China dai na zama kasa da tafi gurbata muhalli a duniya wacce ake ganin tana da abin cewa a taron kolin kan sauyin yanayi da za a fara daga ranar 30 ga watan nan na Nuwamba.