Faransa ta kira jakadanta na Burkina Faso | Labarai | DW | 26.01.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta kira jakadanta na Burkina Faso

Ma‘aikatar harkokin wajen Faransa ta kira jakadan kasar da ke Burkina Faso kan batun wa'adin wata daya da aka ba wa sojojin Faransa na su fice daga kasar.

Kiran jakadan Faransa a Burkina Faso na zuwa ne kwanaki bayan da hulda ta fara tsami tsakanin kasashen biyu, a daidai lokacin da kuma harkar tsaro ke kara tabarbarewa a Burkina Faso, duk da dakarun sojan Faransa sama 400 da ke a jibge a kusa da Ougadougou fadar gwamnatin kasar.

Burkina Faso na zama kasa ta biyu bayan Mali da ta dauki irin wannan mataki na katse huldar soja da Faransa domin karkata alakarta ga kasar Rasha wace sannu a hankali ta fara yi wa wasu kashe renon Faransa dauki daya-daya.

Kamfanin dilancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa daga cikin ababen da za a tattauna da jakadan har da batun ci gaba ko dakatar da tallafin da Faransa ke bai wa Ougadougou, kamar yadda a ka katse wanda ake bai wa Mali mudin Burkina Fason ta kulla hulda da sojojin haya na Wagner na Rasha.