Faransa ta kare tsoma bakinta a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya | Labarai | DW | 11.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta kare tsoma bakinta a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya

Shugaban Faransa, wanda ya isa Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya, ya ce wajibi ne Faransa ta warware rikicin kasar.

Shugaba Hollande na kasar Faransa ya isa Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya, jim kadan bayan da wasu 'yan bindiga suka harbe - har lahira wasu dakarun Faransa biyu. Hollande, ya sauka a Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya ne, bayan halartar taron addu'oin karrama tsohon shugaban Afirka Ta Kudu Nelson Mandela, wanda ya gudana a birnin Johannesburg a wannan Talatar (10.12.13). Dama dai a karshen makon da ya gabata ne Faransa ta kara yawan dakarunta da ke Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya ya zuwa 1,600, wanda shugaba Hollande ya ce yana tattare da hatsari, amma kuma ya zama wajibi ne Faransa ta gudanar da aikin.

Idan za a iya tunawa dai cikin watan Maris ne 'yan tawayen Sekeka da ke da rinjayen Musulmi suka kifar da gwamnatin Francoir Bozize na kasar da mafi yawan al'ummarta ke zama mabiya addinin Kirista.

Ma'aikatan bayar da agaji na cikin gida a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya suka ce sun yi nasarar gano gawarwaki 460, bayan barkewar yaki a tsakanin mayakan sa kai na kungiyoyin Musulmi da na Kirista a ranar Alhamis (05. 12. 13) da ta gabata. Sai dai kuma ana ganin yawan mamatan zai karu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu