Faransa ta halaka wasu ′yan tawaye | Labarai | DW | 14.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta halaka wasu 'yan tawaye

Dakarun kasar Faransa sun kai wani hari kan wasu 'yan bindiga a kan iyakar Mali da Aljeriya inda suka halaka wasu daga cikinsu.

Wani harin da sojojin Faransa suka kaddamar ta sama a arewa maso gabashin kasar Mali, ya halaka wasu masu gwagwarmaya da makamai su 10 a kan iyakar kasar da kasar Aljeriya. Wata majiyar jami'an tsaro ta ce harin na yau Laraba, ya kuma lalata wasu kayayyakin yakin 'yan bindigar ciki har da motocinsu.

Harin dai na daga cikin ayyuka ne na sintirin Barkhane da ke aiki a kasashen Mali da Moritaniya da Nijar da Chadi da kuma Burkina Faso. Dakarun kasar Faransar dai sun dauki kwanaki suna aikin tabbatar da tsaro a arewa maso gabashin kasar ta Mali.

Wasu rahotanni kuma daga kasar Burkina Faso, sun tabbatar da kashe wani jami'in dan sanda tare da jikkata wasu a wani harin na 'yan bindiga a garin Fada N'Gourma.