1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Faransa ta sauki matakan kwantar da Zanga-zanga

Zulaiha Abubakar
December 4, 2018

Firaministan Faransa Edouard Philippe ya sanar da jingine uku daga cikin batutuwan da al'ummar kasar suka yi kuka da su ciki kuwa har da karin kudin harajin mai a kasar.

https://p.dw.com/p/39QWc
Frankreich Gelbwesten-Protest in Paris | Édouard Philippe, Premierminister
Hoto: Getty Images/AFP/L. Marin

Sanarwar ta kara da cewar gwamnati ta dakatar da wannan batu har tsawon watanni shidda,nan gaba kadan firaministan zai sanar da wasu matakan inganta rayuwar kananan ma'aikatan kasar da gwamnati da dauka duk dai don kwantar wa da masu zanga-zanagar hankali,a baya dai an jiyo firaministan na jaddada aniyar gwamnatin kasar ta tabbatar da karin harajin mai don tirsasa wa jama'a su daina amfani da man da ke gurbata muhalli. Da yake maida martani daya daga cikin jagororin zanga-zangar Benjamin Cauchy ya shaida wa manema labarai cewar boren nasu ya fara haifar da nasara duk kuwa da cewar ba su gamsu ba.