Faransa ta ce a miƙa mata ′yan ƙasarta da aka yankewa hukunci a Chadi | Labarai | DW | 27.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta ce a miƙa mata 'yan ƙasarta da aka yankewa hukunci a Chadi

Hukumomin ƙasar Faransa sun bukaci a miƙa Faransawan nan shida da aka yanke musu hukunci a Chadi ga kasar ta Faransa. Wata kotu a Chadi ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru takwas takwas a gidan yari bisa laifin yunƙurin bautad da wasu yara ƙanana,bayan an kama su da laifin satar yara 103 daga Chadi. A watan Oktoba aka tsare membobin ƙungiyar agaji ta Zoes Ark a lokacinda suke ƙoƙarin fita da yaran dukkaninsu yan shekaru ƙasa da goma zuwa turai. Iyayen yaran sun ce sun miƙa yaran nasu ne bisa imanin cewa za a sanya su makaranta ne a wani gari dake gabacin Chadi .