Faransa ta bukaci karin matsin lamba ga Siriya | Labarai | DW | 04.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta bukaci karin matsin lamba ga Siriya

Gwamnatin Faransa ta yi kira ga Iran da ta sa baki dangane da hare-haren da dakarun Siriya suka kaddamar a wajen birnin Damascus fadar gwamnatin kasar.

Shugaba Emmanuel Macron na kasar Fraransa, ya yi kiran takwaransa na Iran Hassan Rouhani da ya matsa lamba ga gwamnatin Siriya dangane da hare-haren da ta kaddama kan fararen hula a gabashin Ghouta.

Cikin wata tattaunawa ta wayar tarho, Shugaba Macron ya bayyana irin nauyin da ke kan Iran na ta tabbatar da yin hakan, ta la'akari da alakar kasar da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta Siriya.

Kiran na Mr. Macron na zuwa ne dai dai lokacin da dakarun Siriya suka kwace kashi daya cikin hudun gabashin na Ghouta, da karfin hare-haren da suka kaddamar makonni biyu ke nan.

Sama da mutune 640 suka mutu, yayin da wasu daruruwan kuma suka tsere daga yankin.