Faransa ta amince za ta bar Burkina Faso | Siyasa | DW | 26.01.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Faransa ta amince za ta bar Burkina Faso

Sojojin Faransa suna shirin ficewa daga Burkina Faso cikin wata guda kamar yadda gwamnatin kasar ta yammacin Afirka ta bukata.

Tun da farko Faransa ta janye sojojinta daga kasar Mali mai makwabtaka da Burkina Faso a watan Agustan 2022, ba kawai saboda kin jinin Faransa ba kadai har ma da tsamin dangantaka da sojojin da suka kwace madafun ikon kasar ta Mali. Antoine Glaser masani kan kasashen yankin Sahel ya yi karin bayani.

"Babu kokwanto matasa suna neman ganin Faransa ta janye sojojinta, wannan ya zama batun siyasa na kasa. Tun lokacin da sojoji suka kwace madafun iko babu wata nasarar da suka samu kan mayaka masu jihadi, shi ya saka suke neman goyon baya daga wajen mutanen kasa ta hanyar cewa dole Faransa ta fice daga Burkina Faso."

A watan Satumban shekarar 2022 matsakaicin hafsan soja Ibrahim Troare ya kwace madafun ikon Burkina Faso a wani juyin mulki karo na biyu sakamakon matsalolin tsaro da ake fuskanta. Tun lokacin babu nasarar da habsan sojan mai shekaru 34 da haihuwa ya samu kan yaki da tsageru masu ikirarin jihadi, sai dai fito na fito da Faransa, inda a birnin Wagadugu fadar gwamnatin kasar ake ci gaba da samun kalaman kin jinin Faransa wadda ta yi wa kasar mulkin mallaka. Magoya bayan gwamnatin mulkin sojan suna yabon Rasha da yawo da tutotcin kasar. Seidick Abba masani ne kan harkokin yau da kullum da ke zaune a Faransa

"Ajiye sojojin tun cikin shekarun 2010. Haka ya fara fiye da lokacin da aka kirkiri ayyukan sauran sojoji irin Barkhane. A lokacin akwai 'yan kasashen Turai da ake garkuwa da su a kasashen yankin Sahel, tun gabanin mamaye yankin arewacin Mali. Inda Faransa take da wannan rukunin sojoji da ke aiki da sojoji kimanin 50 har zuwa 100, kuma sannu a hankali ake ci gaba har zuwa kimanin mutane 400 yanzu."

Duk da sojoji 400 na Faransa ba a samu nasarar kawo karshen hare-haren ta'addancin da ake fuskanta ba a kasar. Kuma idan Faransa ta janye daga Burkina Faso ana ganin kasar za ta dauki mataki irin na makwabciyarta Mali wajen kara hada kai da Rasha ta bangaren aikin soja. Duk yadda ta kasance babbar matsalar kasar Burkina Faso ita ce ta'addanci. Masana sun nuna dari-dari idan Rasha za ta iya taimakon kasar magance wannan babbar barazana yayin da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce harkokin jinkai suna kara sukurkucewa a wannan yankin na Sahel.

Sauti da bidiyo akan labarin