1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Shirin zaben fidda gwani na jam'iiyar Socialist

Salissou Boukari
January 12, 2017

'Yan takara neman shugaban kasar Faransa guda bakoye a karkashin inuwar jam'iyyar da ke mulki ta 'yan Socialist, za su fafata da yammacin ranar Alhamis a wata mahawara ta farko.

https://p.dw.com/p/2VgOb
Frankreich Manuel Valls PK zur Kandidatur in Paris
Tsohon Firaministan kasar Faransa, kuma dan takara Manuel VallsHoto: Reuters/C. Platiau

'Yan takaran dai sun hada da maza shida, da kuma mace guda, inda kowane zai yi kokarin gamsar da 'yan kasar ta Faransa irin manufofinsa kafin zaben fidda gwani da za a yi zagaye na farko na wannan jam'iyyar wanda zai gudana a ranar 22 ga watan nan na Janairu a kokarin da ake na fuskantar zaben shugaban kasar ta Faransa da zai gudana kasa da watanni hudu masu zuwa.

Cikin 'yan takarar akwai tsofon Firaminista Manuel Valls mai shekaru 54 da haihuwa, akwai kuma Arnaud Montebourg tsofon ministan kudin kasar a karkashin gwamnatin ta Fransoi Hollande shima mai shekaru 54 da haihuwa mai rajin nuna kishin kasar, da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Akwai kuma tsaffin ministoci, da tsaffin 'yan majalisar.