1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa na neman dakile rikicin Burundi

Mouhamadou Awal BalarabeNovember 10, 2015

Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya ya nemi a kawo karshen tashin hankali a Burundi ta hanyar ladabtar da masu tayar da wutar wannan rikici.

https://p.dw.com/p/1H3Os
Gérard Araud Botschafter Frankreichs bei der UN
Hoto: DW/S. Mwanamilongo

Kasar Faransa ta yi kira ga sauran takwarorinta na duniya da su yi iya kokarinsu wajen ganin cewar su kawo karshen tashin hankalin da ke iya tsunduma Burundi cikin yakin basasa. A lokacin taron kwamitin sulhu da aka shafe sa'o'i 13 ana gudanar da shi a cibiyar Majalisar Dikin Duniya da ke New-York, ita Faransa ta shigar da wani daftarin doka, wanda ya tanadi hukunta duk wadanda za a samu da hannu wajen ruruta wutar rikicin na Burundi.

Tun dai bayan da kisan dauki dai-dai yake neman zama ruwan dare a Burundi, kasashen duniya suka fara nuna fargaba dangane da yiwuwar sake fadawar kasar cikin yakin basasa. Idan za a iya tunawa dai, Burundi ta yi fama da yakin basasa shekaru 21 da suka gabata, wanda ya yi sanadi asarar rayukan mutane dubu 800 galibunsu kuwa tsiraru 'yan Hutu.

Tun dai bayan da shugaban kasa Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta yin tazarce a watan Afirilu , aka fara sa in sa tsakanin 'yan adawa da kuma magoya bayan gwamnatin ta Burundi.