Faransa: Jana′izar limamin Coci Jacques Hamel | Labarai | DW | 02.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa: Jana'izar limamin Coci Jacques Hamel

A Faransa a wannan Talata ce ake gudanar da jana'izar babban limamin cocin birnin Saint-Etienne-du Rouvray wanda wasu masu da'awar jihadi suka yi wa yankan rago a cikin cocinsa makonni biyu da suka gabata.

Mutane kimanin dubu biyu ne ake sa ran za su halarci taron jana'izar wanda za a gudanar da misalin karfe 12 agogon JMT a babbar Cocin birnin Rouen. Kisan gillar da aka yi wa Jacques Hamel limamin Krista dan shekaru 85 a duniya ya girgiza al'ummar kasar ta Faransa musamman mabiya addinin Krista.

Musulmi da dama a kasar ta Faransa da sauran kasashen duniya sun yi tir da Allah wadai da kisan malamin Kristan wanda aka tabbatar na taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinin Krista da na Muslmi a garin na Saint-Etienne-du Rouvray.