Faransa: Jam′iyyar FN ta lashe zaben lardina | Labarai | DW | 07.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa: Jam'iyyar FN ta lashe zaben lardina

Jam'iyyar Frond National ta Marine Lepen ta lashe zaben lardina a Faransa da kashi 28 daga cikin dari a yayin da jam'iyyar 'yan gurguzu ta Francois Hollande ta zo ta uku da Kashi 23 da digo biyar daga cikin dari.

A kasar Faransa kwana daya bayan lashe tun a zagayen farko zaben lardinan da ya gudana a kasar a karshen mako , jam'iyyar Frond National ta Marine Le pen ta bayyana aniyarta ta lashe zaben shugaban kasa na shekara ta 2017 domin kawo karshen abin da ta kira mummunan milkin da gwamnatin da ke ci a yanzu ta jima tana yi:

"Ta ce a yau ta bayyana fili cewa al'umma ta yi watsi wannan gwamnati wacce ta rigaya ta huke da kuma ba abin da ta kawo wa al'umma illa matsalolin tsaro da na rashin aikin yi da makoma mars tabbas , wanda shi ne ya sanya al'umma ta dauki mataki na kanta a kai"

Jami'yyar FN ta masu ra'ayin kyamar baki ta lashe zaben lardina na kasar ta Faransa da kashi 28 daga cikin dari, jam'iyyar Republicain ta samu kashi 27 daga cikin dari a yayinda jami'yyar Shugaban mai ci Francois Hollande ta zo ta uku da kashi 23 da digo biya daga cikin dari.