Faransa da Jibouti sun sake tsawaita yarjejeniyar tsaro
July 25, 2024Talla
Kasashen Faransa da Jibouti sun sake cimma yarjejeniyar tsaro bayan kwashe shekaru biyu ana kai komo. A cewar wata majiya da ke kusa da masu tattaunawa, an samu jinkiri ne sakamakon bukatar Jibouti na neman Faransa ta kara kudin hayan da take biya domin girke sojojinta.
A cikin sanar da fadar shugaban kasar Faransa ta fitar, ta ce yarjejeniyar da aka saka hannu a kanta a offishin Shugaba Macron, na kunshe ne da kasancewar dakarun Faransa 1,500 a karamar kasar da ke gabashin Afirka. Tun dai a shekarar 1977 ne aka fara sanya hannu kan wannan yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro tsakanin kasar Jibuti da uwargjiyarta Faransa tare da sabunta ta a shekarar 2011.