1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: An dage haramci kan Burkini

Abdulahi Tanko BalaAugust 26, 2016

Kotu a Faransa ta dage haramci da a baya wasu birane suka sanya kan kayan nan na ninkaya da Musulmi ke sanyawa wanda ake kira Burkini.

https://p.dw.com/p/1Jqoj
Frankreich Korsika Frau mit Burkini im Meer
Hoto: picture-alliance/abaca

Kotun kolin Faransa ta jingine haramcin sanya tufar Burkini ta ninkaya da ke rufe dukkan jiki wadda hukumomin gundumomi a Faransar suka sanya. Ita dai tufar ta Burkini galibin mata Musulmi ne ke sanya ta. Hukumomin gundumomin sun ce sun dauki matakin haramta Burkini ne saboda karuwar damuwa game da ayyukan yan ta'adda.

Sai dai haramcin ya harzuka Musulmin da masu rajin kare hakkin bil Adama a Faransar. A yanzu dai hukuncin kotun kolin na jingine haramci a kan tufar ta Burkini zai share fagen neman dage dokar a wasu garuruwan Faransar fiye da 30 wadanda su ma suka hana sanya tufafin. Mai yiwuwa hakan ba zai kawo karshen takaddama kan matsanancin halin da Faransa ta shiga ba game da sajewar Musulmi a rayuwar kasar ta yau da kullum ba.