1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

191110 Bemba Prozess

November 22, 2010

Lauyoyin Bemba sun ce bashi da laifi da zargin da ake masa

https://p.dw.com/p/QExb
Hoto: AP

A yau ne ake fara sauraron shari'ar tsohon mataimakin shugaban Janhuriyar Demokraɗiyyar Kongo Jean-Pierre Bemba a kotun hukunta masu miyagun laifukan yaƙi da ke birnin Den Haag. Ana zargin tsohon madugun 'yan tawayen ne dan gane da irin rawa daya taka a yaƙin janhuriyar Afrika ta Tsakiya dake makwabtaka.

" Ina jiran goyon bayan al'ummar Kongo, domin samun nasara., tare da samar da sabuwar alqiblar gudanarwar gwamnati a Kongo"

Waɗannan kalaman Jean-Pierre Bemba ke nan a lokacin da ake gudanar da zaɓen shugaban kasa a ranar 30 ga watan Yulin 2006. A lokacin yana ganin nan bada jimawa ba shi ne zai kasance shugaban kasa a janhuriyar demokradiyyar Kongo. Sai da sakamakon zaɓen ya kasance daban, inda abokin takararsa Joseph Kabila ya lashe. Daga nan ne Bemba ya ji tsoron rayuwarsa, wanda ya jagonce shi gudun hijira zuwa ƙasar Poturgal a watan Aprilun 2007. A watan Mayun 2008 ne 'Yan sanda suka cafke shi, kana aka jefa shi a Kurkuku a watan yuni, kusa da birnin Den Haag.

A yau ne dai ake saran gurfanar da Jean-Piere Bemba a gaban kotun sauraraon manyan laifuffukan na ƙasa da ƙasa.

Kongo Hilfe für die Opfer der Gewalt im Ostkongo
Hoto: picture-alliance/dpa

Masu shigar da kara na zarginsa da miyagun laifuffuka na yaƙi da kuma tozartawa bil'adama, waɗanda suka haɗar da kisan gilla, azabtarwa da Fyaɗe. Dakarun Sojansa na MLC ne suka aiwatar da waɗannan miyagun laifuka da suka shafi har kanana yara Mata da basu shige shekaru takwas da haihuwa ba, a tsakanin watannin Oktoban 2002 da Maris ɗin 2003, a janhuriyar Afrika ta tsakiya dake makwabtaka da Kongo. Ga waɗanda aka yi wa wannan cin zali dai, yau ɗin na mai kasancewa babbar ranar farin ciki ce a garesu. Marie-Edith Lawson ce ke wakiltarsu.

"Duk da cewar ba za'a iya biyan diyyan da zai shafe wannan tozartawa ba, yana da muhimmanci waɗanda aka yiwa laifin sun samu bayanin gaskiyar abubuwan da suka wakana a lokacin, tare da samun damar tofa albarkacin bakin su kan halin da suka kasance a ciki. Ya zamanto wajibi a hukunta masu laifin, domin hakan zai daɗaɗa wa waɗanda aka tozartawan".

Gebäude des Internationalen Strafgerichtshofs Den Haag
Kotun den HaagHoto: dpa

Ga magoya bayan tsohon shugaban Kongo Jean-Piere Bemba dai bashi da laifi ko kaɗan. Duk da cewar Dakarunsa ne suka aiwatar da laifuffukan da ake zargi acewar lauyansa Aime Kilolo.

" kafin mu yi maganar laifuffukan, dole ne mu tabbatar da wanene ya jagoranci sojojin a Bangui tsakanin watannin Oktoba 2002 zuwa Maris 2003, amma ba shugaban sojojin MLC na kasa baki ɗaya ba. Anan matsayinmu a bayyana yake, gwamnatin janhuriyar Afrika ta tsakiya ta nemi tallafin Sojojinmu. Akan haka ne aka aike da waɗannan sojojin, dan haka ba za'a iya cewar jean-Piere Bemba dake jagorantar rundunar sojin na wajen ba".

To sai ga masu shigar da kara dai wannan bashi da tushe. Wakiliyar waɗanda aka tozartawa Marie-Edith Lawson, ta ce kasancewar ba ya wurin da aka aiwatar da laifin, ba zai wanke shi daga tuhuma ba, domin Dakarunsa ne. Takardar zargin Bemba dai na nuni da cewar, a wancan lokaci shine comandan rundunar Sojin Kongo, wanda kuma shine uwa uba ga dukkan ayyukansu.

Mawallafiyya: Kotze, Konstanz /Zainab Mohammed Abubakar

Edita : Mohammad Nasir Awal