Fara jana′izar sarkin Tailan | Labarai | DW | 14.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fara jana'izar sarkin Tailan

Ana shirye-shiryen jana'izar marigayin Sarkin Tailan wanda ya shafe shekaru 70 kan gadon sarauta kuma ake girmama.

An fara shirye-shiryen jana'izar Marigayi Sarki Bhumibol Adulyadej na Tailan inda aka fito da gawar marigayin daga asibin birnin Bangkok fadar gwamnatin kasar tare da wucewa da ita ta gaban duban matane masu zaman makoki da suke nuna alhini. Dan sakin wanda zai gaji kujerar mulkin Yarima Vajiralongkorn yake jagontancin lamuran jana'izar.

Marigayin ya zama sarkin mafi dadewa kan karagar mulki a duniya kafin mutuwa yana da shekaru 88, kuma bayan mulki na shekaru 70 ya zama mutumin da ake girmama a ciki da wajen kasar, wanda yake taka muhimmiyar rawa kan ci-gaba da samun zaman lafiya a kasar ta Tailan wadda take fuskantar rikicin siyasa da juyin mulki na sojoji.