Fara farautar bakin haure a Amirka | Labarai | DW | 15.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fara farautar bakin haure a Amirka

Jami'an hukumar shige da fice na Amirka sun kaddamar da shirin tisa keyar bakin haure marasa takardun shaidar izinin zama a cikin kasar, amma shirin na fuskantar adawa daga wasu mahukunta.

Shugaba Donald Trump ya ce iyalai kusan 2,000 da ke zama a Amirka ba bisa ka'ida ba, na zaman dalilin da ya sanya daukar matakin kame su tare da mayar da su inda suka fito, matakin kuma da tuni aka fara aiawatar da shi a biranen Los Angeles da New York da Chicago da kuma Houton.

Trump ya fifita batun bakin hauren yayin da ya kaddamar da gangamin yakin neman zabensa a wa'adi na biyu na mulkin Amirkan. Sai dai shirin na fuskantar tirjiya d arashin samun hadin kan mahukunta a wasu biranen kasar.