Fanta Diallo - ′Yar fafutuka kuma abar koyi daga kasar Senegal | Himma dai Matasa | DW | 26.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Fanta Diallo - 'Yar fafutuka kuma abar koyi daga kasar Senegal

Dubban matasa ne a kasar Senegal ke kokari ko ta halin kaka wajen ganin sun tsallake daga kasar zuwa kasashen Turai dan neman rayuwa mai inganci.

Fanta Diallo 'yar fafutuka tana ganin sadaukar da rai da matasan Senegal ke yi dan shigowa Turai ba ta dace ba, hakan ya sanya ta kafa wata kungiya mai fadakar da matasan su zauna a kasarsu ta haihuwa.

Wuri mai dinbin damarmaki wannan shi ne birnin Dakar a fadar Fanta Diallo, wacce ta amince cewa akwai makoma mai kyau a kasarta ta Senegal, akidar da take son ta cusa wa matasa a zukatansu. A sabili da haka ne Diallo 'yar shekaru 31 ta kafa kungiyar Senegalese Dream wacce ke kokarin karfafa gwiwar matasa 'yan Afirka su dangana da kasar ta Senegal ba wai kasashen Turai ba.

"Idan matashi ya kasance yana da ilimi ba kamar sauran matasa ba a Senegal, amma sai ya kasance cewa bai samu aiki ba, mai ya kamata yayi, ya fice daga kasar? Ya kwanta yana bacci ? A'a tashi tsaye ka ga mai za ka iya yi ka yi shi."

Daya daga cikin irin wadannan matasa na zama makwabcin Fanta Diallo wato Bouka wanda ta tallafa masa ya samu shago da yake sayar da kofi.

"Na rubuta ne a kan takarda na gabatar musu da bukatata , sai suka bani shawara na yi kaza na bar kaza, hakan zai taimaka min. Haka kuma aka yi suka taimaka min da wurin da zan zauna na yi wannan sana'a ta saiyar da shayi."

Dubban matasa ne dai masu ilimi ke kokari su fice daga Senegal dan neman aiki a kasashen waje, inda suke ketara tekun Bahar Rum ta amfani da jiragen ruwa marasa inganci. A cewar kungiyar da ke lura da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa, tsakanin watan Janairu zuwa watan Maris an samu 'yan Senegal 1200 da suka isa gabar teku a Italiya. Amma kungiyar ta Senegalese Dream ta yi nasara wajen sauya tunanin Bouka tare da tallafa masa ya zamo mai dogaro da kansa bayan tsara masa shawarwari da za su kai shi ga tudun mun tsira.

Bouka Sy

Bouka Sy matashi da ke jin shawarar Fanta Diallo

Fanta kan je makarantu a sassa daban-daban na kasar dan ganin ta fadakar da matasa da ma koya musu sana'o'i da basu karfin gwiwa kan ayyukan gona wadanda a cewarta su ne mafita ga matsalolin rashin aikin yi da matasa ke fama da su a garuruwansu na haihuwa.

"Mutane sun gwammace su rika sharar titi a biranen Amsterdam ko Berlin ko Bercelona sabanin su yi aiki a kasarsu ta haihuwa. Idan sun dawo birnin Dakar su sanya kaya masu kyau 'yan uwansu su tarbesu a filin tashi da saukar jiragen sama. Su duba cikin 'yan mata a garinsu da suka fi kyau su yi aure, wata guda baya su koma birnin Berlin su ci gaba da sharar titi."

Fanta Diallo Zuhörer Zuschauer

Matasa masu sauraron laccar fanta Diallo

Yara da dama dai Fanta ta zame musu gwarzuwa abar koyi a garesu inda suke fatan zama tamkarta kamar yadda wannan daliba ke cewa.

"Fanta ta zamo abin koyi a gareni, ina so na zama kamarta idan na kammala makaranta."

Irinsu Fanta dai da iyayensu suka so su yi aiki a kasashen Turai koma dai a ce a Faransa. Bayan samun horo a Turai ta koma gida inda a kullum take karbar koke-koken jama'a na son danganawa da Turai dan samun kyautatuwar rayuwa.

Sauti da bidiyo akan labarin