Falasdinu ta mika kokenta ga kotun ICC | Labarai | DW | 26.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Falasdinu ta mika kokenta ga kotun ICC

Ministan harkokin kasashen ketare na Falasdinu Riad Malki ya mika wani kundi ga kotun hukunta masu aikata manyan laifukan yaki ta kasa da kasa wato ICC.

Riad al-Malki ministan harkokin kasashen ketare na Falasdinu

Riad al-Malki ministan harkokin kasashen ketare na Falasdinu

Kundin dai na kunshe ne da shaidun da zasu tabbatar da zargin kisan kiyashi da suke yiwa Isra'ila a farmakin da ta ke kaiwa a yankin Zirin Gaza da kuma Gabar Yamma da Kogin Jodan. A yanzu haka dai mai gabatar da kara ta kotun Fatou Bensouda za ta fara gudanar da binciken sharar fage domin tabbatar da zargin Isra'ila da aikata laifukan yaki a Falasdinun. Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar ya zargi Isra'ila da Falasdinu da yiwuwar aikata laifukan yaki a yayin yakin da suka gwabza da juna a yankin Zirin Gaza a shekarar da ta gabata ta 2014. Tuni dai Isra'ilan ta yi watsi da wannan batu tana mai cewa ita ba mamba ba ce a kotun ta ICC.