Falasɗinawa na yin zaɓukan magadan gari | Labarai | DW | 20.10.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Falasɗinawa na yin zaɓukan magadan gari

Falasdinawa sun fara gudanar da zabuka na magadan gari a gabar yamma ta kogin Jordan inda ake sa ran kimanin mutane rabin miliyan za su kaɗa kuri'unsu.

Da misalin ƙarfe biyar na safiyar yau ne dai agogon GMT aka buɗe rumfunan zaɓe a yanki kuma ana sa ran kammala shi da misalin ƙarfe biyar na yamma agogon na GMT kana sakamakon farko na zaɓen zai bayyana da sanyin safiyar gobe lahadi idan Allah ya kaimu.

Kimanin 'yan takara dubu huɗu da dari bakwai wanda kashi ashrin da biyar daga cikinsu mata ne za su fafata a zaben wanda shi ne irinsa na farko cikin shekaru shiddan da su ka gabata.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

 • Kwanan wata 20.10.2012
 • Muhimman kalmomi PLS
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16ToB
 • Kwanan wata 20.10.2012
 • Muhimman kalmomi PLS
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16ToB