Fahintar juna da Amurka kan kasuwanci | Labarai | DW | 13.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fahintar juna da Amurka kan kasuwanci

Jamus da Canada da Japan za su ci gajiyar bunkasar kasuwancin Amurka, wanda hakan ya sa suka sanar da amincewa da sabbin manufofin gwamnatin Donald Trump kan kasuwanci da haraji.

Sakataren harkokin kudi na kasar Amurka Steven Mnuchin ya sanar da cewar manyan abokan huldar kasuwanciAmurka sun yi aman da tsarin kasuwanci da harajin gwamnatin Donald Trump, kasancewar zasu ci gajiya daga shirin bunkasar tattalin arikin Amurka.

Mnuchin ya yi wannan furuci ne bayan ganawarsa da manyan abokan kasuwancinsu da suka hadar da Jamus da Japan da Canada, a gefen taron ministocin kudi na kasashe masu cigaban masana'antu na G7 a Bari da ke kasar Italiya.

Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan harkokin kudi da batutuwan tsaro, da ya kunshi daukar matakai kan masu kaucewa biyan haraji na kasa da kasa, da kuma tunkarar barazanar kai farmaki ta yanar gizo da kasashen duniya ke fama da ita, kamar yadda ya kasance a ranar juma'a.