Fagen siyasar Najeriya ya kama hanyar sauyawa | Siyasa | DW | 01.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fagen siyasar Najeriya ya kama hanyar sauyawa

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC, ta amince da yiwa jam'iyyar adawa ta APC rajista, wadda za ta kalubalanci jam'iyyar PDP a zabukan 2015.

Attahiru Jega, Independent National Electoral Commission Chairman, reads the results sheet before he declared Nigeria's incumbent President Goodluck Jonathan as the winner of last Saturday's presidential election, in Abuja, Nigeria, Monday, April 18, 2011. Jonathan clinched the oil-rich country's presidential election Monday, as rioting by opposition protesters in the Muslim north highlighted the religious and ethnic differences still dividing Africa's most populous nation. (AP Photo/Sunday Alamba)

Wahlen Nigeria Ergebnis

A yanayin da ke nuna kama hanyar sauya fagen siyasar Najeriyar hukumar zaben kasar ta sanar da yi wa babban jam'iyyar adawar nan ta All Progressive Congress wato APC a takaice, rijista bayan kwashe wata guda cur tana jiran faruwar hakan.

An dai kafa tarihi a Najeriyar domin kuwa wannan ne karon farko da manyan jami'yyun adawar kasar suka yi watsi da bambamci da ke tsakaninsu suka hade wuri guda don tunkarar jami'yyar PDP mai mulki. Domin sanar da rijista ga jam'iyyar ta APC da hukumar zaben Najeriyar ta yi ya zama ba-zata ga mutane da dama saboda dogon lokacin da aka kwashe ana ta nuku-nukun ko za ta samu rijistar duk da cewa ta cika dukkanin ka'idojin da ake bukata ga kowace kungiya da take son zama jam'iyya a kasar.

Büro der Oppositionspartei Actopm Congress of Nigeria in Abuja, Address No. 16, Bissau Street, Wuse Zone 6, Abuja *** Bild von DW-Mitarbeiter Ubale Musa, 28. Januar 2013

Shelkwatar jam'iyyar ACN a Abuja

Ko da yake hukumar zaben Najeriyar ta ce jam'iyyar ta cika dukkanin ka'idoji abin da yasa aka yi wa APC din rijista, to ko ina aka kwana da kungiyar African Progresive da ta nufi kotu a kan cewa ita ce ke da wannan suna. Mr Nick Dazan shi ne jami'in yada labaru na hukumar zaben Najeriyar.

Maraba da wannan ci-gaba

Tuni dai 'ya'yan jam'iyyun da suka hada kai suka kafa jam'iyyar suka shiga murnar samun rijistar da suke ganin tamkar yau take sallah a garesu. Malam Faruq Adamu Aliyu shi ne shugaban kwamitin ladabtarwa na tsohuwar jam'iyyar CPC.

Shi kuwa Comrade Sabo Muhammad ya ce "rijista ga jam'iyyar kafa tarihi ne ga demukradiyyar Najeriyar."

Ba girin-girin ba, ta yi mai

Former Nigeria military dictator and presidential candidate for the Congress for Progressive Change (CPC) retired General Muhammadu Buhari speaks on the April elections in Lagos on March 15, 2011. Nigeria holds presidential, state and legislative elections in April in a test to see if it will break with its history of deeply flawed and violent polls. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)

Muhammadu Buhari jigo a tsakanin 'yan adawar Najeriya

To sai dai ga Malam Lawali Shuaibu sakataren jam'iyyar ACN da ta rikide ta koma jam'iyyar APC a yanzu ya ce "duk da cewa suna cike da murna da farin cikin samun rijista da za ta canza yadda ake gudanar da harkar siyasa a Najeriya, to amma wannan kalubale ne a garesu domin ba girin-girin ba."

A yanzu kalubale ya koma ga 'ya'yan wannan sabuwar jam'iyya da ta kama hanyar sauya guguwar da ke kadawa a fagen siyasar Najeriyar, domin dimbin magoya bayansu da za su sa ido don ganin ko za su ba mara da kunya domin bambamce aya da tsakuwa.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin