Fafutukar yaki da ta′addanci a yankin Sahel | Labarai | DW | 13.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafutukar yaki da ta'addanci a yankin Sahel

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sanar da cewar Saudiyya za ta ba da gudunmowa miliyan dari na dala, domin yaki da ta'addanci a yankin Sahel.

A taron da aka gudanar a kusa da birnin Paris, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce dole ne, su samu nasara a yakin da 'yan ta'adda a yankin Sahel. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da firaministan Italiya Paolo Gentiloni na daga cikin wadanda suka halartarci taron.