Fafutukar kawo karshen Ebola | Siyasa | DW | 01.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fafutukar kawo karshen Ebola

A Najeriya an gudanar da taron gaggawa kan cutar Ebola domin daukar sababbin matakan shawo kan cutar, musamman dakile yaduwarta zuwa sauran jihohi da ma kan iyakokin Kasar.

Daukan sababbin matakai na gaggawa a game da wannan mumunar annoba ta cutar Ebola, ya biyo bayan fuskantar kalubale a fanin kula da sa ido a kan mutanen da ake kebe da su ana ci gaba da yi musu gwaji domin tabbatar da cewa basu da wannan cuta, abinda tserewar daya daga cikinsu ya haifar da samun bullar cutar a garin Fatakwal a makon jiya.

Kiran taron gaggawa kan Ebola

Wannan ya sanya kiran taron gaggawa domin sake shata sababbin dubarun da za a dauka a daukacin jihohin Najeriyar da ma kan iyakokin kasar. Ministan kula da lafiya na Najeriyar Farfesa Onyebuchi Chukwu ya bayyana cewa dubarun da suka sa a gaba sune na ilmantarwa da wayar da kan jama'a da kuma samar da bayanai. Dr Khaliru Alhassan shine ministan kasa a ma'aikatar lafiya ta Najeriya ya bayyana matakan da ake dauka a kan matsalar ta cutar ta Ebola.

Halin yanayi na firgici da rashin yarda da ya shiga cikin zukatan jama'a a game da cutar na zama wata matsala da jami'an kula da lafiya suka yi gargadin kaucewa yada bayanai na karya da kauce nuna kyama ga masu lalurar. Dr Sani Labaran na cikin tawagar jihar Sokoto da suka hallarci taron ya bayyana mana matakan da aka amince za a dauka a jihohin domin dakile matsalar cutar ta Ebola.

Akwai bukatar kara wayar da kan al'umma.

Kwararru dai sun bayyana cewa aiki yafi yawa a matakan jihohi da kanana hukumomi inda a nan ne jama'a da yawa suke a zaune da ke bukatar bayanai a kan cutar, domin samun ilimin kariya a matakin farko daga cutar Ebola. Ya zuwa yanzu dai mutane 199 ne ake sa ido a kansu domin tabbatar da ko suna da cutar ta Ebola, yayin da mutane biyar suka mutu. Rahotannin sun bayyana cewa mutane 16 da suka kamu da cutar na samun sauki sosai. Abin jira a gani shine samun nasarar dakile cutar kamar yadda mahukuntan Najeriyar ke fatan gani.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar/ USU

Sauti da bidiyo akan labarin