Fafutukar cimma maradun ƙarni a Najeriya. | Zamantakewa | DW | 25.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Fafutukar cimma maradun ƙarni a Najeriya.

A na daf da kai ƙarshen wa'adin da aka ware na cimma maradun ƙarni wato MDG a shekarun 2015, sai dai har yanzu da saura a fannoni da dama a Najeriya.

Manyan abubuwan da ake mayar da hankali akan su na maradun ƙarni guda takwas sune : rage yawan talauci, da inganta sha'anin illimi, da kiwon lafiya, da sha'anin noma da kiwo , da yaƙi da ciwon SIDA, da rage yawan mutuwar yara ƙanana, kana kuma da samar da yanayin gewayen ɗan adam mai kyau,da dai sauran su.

Bauer mit Bewässerungsanlage für den Maisfeld in Kwadiya Dorf bei Dutse, Jigawa, Nigeria. 29.03.2013, Kwadiya, Jigawa / Nigeria Copyright: DW

Masu aikin gona

Ƙasashen duniya manbobin Majalisar Ɗinkin Duniya guda 193 da wasu ƙungiyoyin masu fafutuka 23 suka haɗu suka rataɓa hannu akan wannan yarjejeniya a birnin New York, na Amurika a shekarun 2000.

To amma misali Tarrayar Najeriya da ke ɗaya daga cikin ƙasashen da suka amince da shirin har yanzu rayuwar al'umma na daɗa yin muni. Ga yuwan ga talauci, sannan babu issasun magunguna a asibitoci, kuma filayen da ake noma wa na ƙara ja da baya. Shin ko za a iya cimma wannan ɓuri kafin shekarun na 2015, wannan ita ce tambayar da na yi wa Adamu Mohammed wani jami'in da ke kula da shirin a Jigawa.

Ya ce: ''Ƙasashe kamar namu ko da an cimma shirin ɗari bisa ɗari, ba zai yiwu ba a kwatantasu da ƙasashen da suka ci- gaba.''

Najeriya dai mai yawan al'umma sama da miliyan ɗari , jama'a da dama ne ke yin rayuwa da ƙasa da dalla Amurika ɗaya a yini, abinda ke zaman koma baya ga ci gaban tattalin arzikin ƙasar da kuma na jin dadin rayuwar al'ummar. Jahar Jigawa dai na ɗaya daga cikin jihohin Tarrayar Najeriya da ake ƙaddamar da shirin na MDG

Mawallafiya : Zainab Shuaib Rabo
Edita : Abdourahamane Hassane