1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutikar neman zama firaminista a Birtaniya

Nigel TandyMay 7, 2010

Shugabanin jam'iyu mafi girma na ƙasar Birtaniya sun fara neman ƙulla ƙawance da ƙananan jam'iyu domin samun damar kafa gwamnatin haɗin gambiza.

https://p.dw.com/p/NJ2V
Majalisar BirtaniyaHoto: AP

ƙasar Birtaniya ta kama hanyar samun gwamantin haɗin guywa biyowa bayan rashin samun rinjaye a majalisa da babbar jam'iyar adawa ta Conservetives ba ta yi ba. Sakamakon ƙuri'un da aka kaɗa ya nunar da cewa jam'iyar da David Cameron ke shugabanta ta lashe kujeru 306-yayin da ta Labour ta firaminista mai barin gado ta tashi da kujeru 258. Ita kuwa jam´'iyar Liberal Demokrats ta sami kujeru 57-yayin da sauran ƙananan jam'iyun suka lashe kujeru 28.

 Madugun 'yan adawan na Birtaniya wato David cameron ya nunar da cewa jam'iyarsa ta fara tattaunawa da ta Nick Klegg domin duba yiwuwar kafa gwamnatin haɗaka. Shi kuwa Gordon Brown da jam'yarsa ta Labour ta yi asarar kujeru 90 , ya nuna cewa a shirye ya ke ya ƙulla ƙawance da wasu jam'iyu domin samun damar kafa gwamnati ta gaba.

Hukumar zaɓen ƙasar ta Birtaniya ta baiyana cewa za ta gudanar da bincike domin gano dalilan da ya sa ba a bai wa ɗaruruwan 'yan ƙasar damar kaɗa ƙuri'arsu a jiya ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu