1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutikar kare birrai a Kamaru

Moki Kindzeka/Yusuf Ibrahim/ YBApril 20, 2016

Nimpa Clement na daya daga cikin masu cin birrai ya bayyana cewa a danginsu suna jin dadin cin naman biri dan haka suke halartar duk inda ake siyar da namansa.

https://p.dw.com/p/1IZ3q
Wasserkraftwerk am Kongo
Birrai dai an tasamma karar da su a wasu kasashe na AfirkaHoto: picture alliance / dpa

A kasar Kamaru ana ci gaba da farautar namun daji musamman birrai a matsayin sana'a haka ne ya sa wata mai suna Anougue France 'yar shekaru 28 da haihuwa ke karfafa wa mutane gwiwar yin mu'amala da dabbobin a madadin farautarsu a wani wuri inda aka kebe dan birrai da giwaye mai suna Campo.

Anougue France dai ta kwashe kusan watanni shida a kebabben wuri da aka ware wa dabbobin kuma ba ta da niyyar barin wurin har sai ta cimma manufarta ta ganin mutane sun fahimci fafutikarta. Kuma ta samu nasara sosai wajen karfafa wa mutane gwiwar ba da manufar samun kudi ba.

Nimpa Clement na daya daga cikin masu zuwa gidan abinci na " Afrikan Climate restaurent " dan cin naman biri ya bayyana ra'ayinsa game da naman cewa:

Kongo Kisangani Bushmeat auf dem Markt
Kasuwancin naman birraiHoto: picture-alliance/AP Photo/S. van Zuydam

"Ni duk dangina suna sha'awar naman biri saboda da matukar muhimmanci ga gina jiki".

Ita dai Anougue da ke fafutikar ganin ta kare hakkin dabbobin ba tare da an muzguna musu ba ta bayyana irin yadda ya kamata al'umma su rika mu'amala da dabbobin.

"Abu ne me sauki ka hadu da birrai, idan ka saba da su ta hanyar wani sauti ko wata alama ko kuma ta hanyar taba hannuwanka, yin haka zai iya sawa ka ga suna kwai- kwayonka kuma yin hakan zai sa ka ga sun saba damu harma su rika zuwa kusa da mu ba tare da jin tsoro ba".

Affe
Wasa da biri kan zamo abin sha'awaHoto: dapd

A kasar Kamaru dai ana farautar birrai ne a matsayin namun daji, kananan kuwa akan sayar da su ga al'umma dan su yi kiwo a matsayin abun sha'awa. A yanzu dai hakan ya zama sana'ar da ake samun kudade a kasar.