Fafaroma zai tattauna da shugabannin addinai na Kirista | Labarai | DW | 24.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma zai tattauna da shugabannin addinai na Kirista

Fafaroma Francis zai fara wata ziyara ta kwanaki uku a yau a yankin Gabas ta Tsakiya, inda zai gana da shugabannin darikun addinin Kiristan da ke yankin

Ziyara wace ke da manufar samar da kafa ta tattaunawa tsakanin addinai na Kirista na Katholika da Orthodox waɗanda ke da rarrabuwar kawuna. Za ta kai jagoran ɗarikar Roman Katolikan a ƙasashen Jordan da Isra'ila da kuma Gaɓar Gokin Jordan.

Hukumomi a ƙasar ta Isra'ila sun ƙarfafa tsaro tare da baza 'ya sanda sama da dubu takwas domin tabbatar da tsaro.Ana sa ran a wannan ziyara Fafaroma Francis ɗin yai kuma tattauna da wasu shugabannin addinai na musulmai.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Pinado Abdu Waba