1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar matasa su kansace masu juriya

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 31, 2016

Babban jagoran Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya bukaci matasa 'yan darikar, da su kasance masu juriya domin su shawo kan matsalolin da duniya ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/1JZHX
Fafaroma Francis yayin taron matasa a Polan
Fafaroma Francis yayin taron matasa a PolanHoto: picture-alliance/dpa/A. Weigel

Fafaroma Francis ya yi wannan kiran ne a yayin bikin rufe taron bikin matasa na duniya da aka kammala a kasar Poland. Tun da fari Fafaroman ya bukaci matasan Kiristocin mabiya darikar Katolika da su kasance masu zama kan teburin tattaunawa da yaki da kalaman nuna kyama da kuma son zuciya. An dai gudanar da bukuwan matasan na duniya ne a dandalin "Field of Compassion" da ke Krakow a kasar ta Poland. A cewar Fafaroma Francis za a gudanar da taron matasan na duniya mai zuwa a Panama a shekara ta 2019.