Fafaroma ya buƙaci a dakatar da yaƙe-yaƙe | Labarai | DW | 25.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma ya buƙaci a dakatar da yaƙe-yaƙe

Jagoran Ɗarikar Roman Katolika Fafaroma Francis ya bukaci da a daktar da yaƙi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da Sudan ta Kudu, da kuma wasu sauran ƙasahen duniya.

Fafaroma ya bayyana haka ne a lokacin wani jawabin da ya saba yi na bukukuwan sallar kirisimeti a dandanlin Saint Pierre zuwa ga mabiya ɗarika Katolikan na duniya baki ɗaya.

A lokacin da yake yin jawabin ya ce za su ci-gaba da yin ad'u'oi ga ƙasar Siriya da Iraki waɗanda ke fama da tashe- tashen hankula. Sannan kuma ya bayyana damuwarsa dangane da lamarin saka yara ƙanana waɗanda shekarunsu ba su kai ba a cikin aikin soji.

Mawallafin : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe