Fafaroma ya buƙaci a dakatar da yaƙe-yaƙe
December 25, 2013Talla
Fafaroma ya bayyana haka ne a lokacin wani jawabin da ya saba yi na bukukuwan sallar kirisimeti a dandanlin Saint Pierre zuwa ga mabiya ɗarika Katolikan na duniya baki ɗaya.
A lokacin da yake yin jawabin ya ce za su ci-gaba da yin ad'u'oi ga ƙasar Siriya da Iraki waɗanda ke fama da tashe- tashen hankula. Sannan kuma ya bayyana damuwarsa dangane da lamarin saka yara ƙanana waɗanda shekarunsu ba su kai ba a cikin aikin soji.
Mawallafin : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe