1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma na ziyara a Siri Lanka

January 13, 2015

Ziyarar da ya kai wannan kasa na zama karon farko cikin shekaru 20 da wani Fafaroma ke ziyarar Siri Lanka bayan kwashe shekaru sama da talatin na yakin basasa.

https://p.dw.com/p/1EJGP
Papst Besuch in Sri Lanka 13.01.2015
Hoto: Ishara S. Kodikara/AFP/Getty Images

Fafaroma Farancis ya bukaci gwamnatin kasar Siri Lanka ta zamo mai mutunta dokokin kasa da kasa da suka shafi hakkin bil Adama, inda ya bukaci a tabbatar da ganin an shigar da gaskiya wajen lamuran da suka shafi binciken yakin basasar kasar.

Fafaroma Farancis ya bayyana wannan bukata ne a ziyarar da ya kai wannan tsibiri karon farko cikin shekaru 20 da wani Fafaroma ke ziyarar wannan kasa.

Ya ce gaskiya na kasancewa wani bangare na samun waraka a kowane abu saboda haka yin ta kan binciken rikicin da kasar ta kwashe na tsawon shekaru 37 zai taimaka wajen ci gaban murmurewar da kasar ke yi bayan gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan awaren Tamil.

Kasar dai ta Siri Lanka ta ki amincewa ta bada hadin kai ga sauran kasashe kan bukatun Majalisar Dinkin Duniya dan gudanar da bincike kan ayyukan take hakkin bil Adama kan fararen hula a rikicuin da kasar ta fiskanta a shekarun baya.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu