Fafaroma Francis: A yi hattara da batun birnin Kudus | Labarai | DW | 06.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma Francis: A yi hattara da batun birnin Kudus

Jagoran darikar Roman Katolika Fafaroma Francis ya yi gargadin da a kiyaye matsayin da birnin Kudus yake da shi, tare da yin hattara da kuma nuna datako a game da wannan batu.

Fafaroman wanda ya bayyana haka daf da lokacin da shugaban Amirka Donald Trump ke shirin bayyana birnin na Kudus a matasayin babban birnin Isra'ila. Ya ce birnin Kudus shi ka dai shi ke, birnin na Yahudawa da Musulmi da kuma Kirista wadanda ko wane ke bauta wa addininsa. MDD da China da Birtaniya sun bayyana fargabansu a game da matakin da shugaban Amirka yake shirin dauka.