1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Babu alamar tsagaita wuta

Ramatu Garba Baba
October 20, 2019

Babu alamar mutunta dokar tsagaita bude wuta a yarjejeniyar da gwamnatin Turkiyya ta cimma da bangaren mayakan Kurdawa kan dakatar da fadan da suke da juna a Siriya.

https://p.dw.com/p/3RaVC
Syrian National Army
Hoto: picture-alliance/AA/B. Kasim

Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Turkiyya ce ta sanar da mutuwar sojanta guda a wani hari da mayakan 'yan tawayen Kurdawa suka kai kansu a kasar Siriya. Sanarwar ta kara da cewa, an budewa rundunarta wuta ba tare da mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da bangarorin biyu masu fada da juna suka cimma ba.

A ranar Alhamis da ta gabata ne, gwamnatin Turkiyyan ta amince ta dakatar da farmakinta a arewacin Siriya na kwanaki biyar don bai wa mayakan Kurdawa damar janyewa da kuma samar da wani sansani da za a tsugunar da 'yan gudun hijirar Siriya sama da miliyan uku da suka tsallaka Turkiyya.