1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fadakar da Bebaye a Kano

August 15, 2017

Bebaye a Kano sun yaba da gudummawar da suke samu daga wata marubuciyar littattafan harshen Bebaye na kasar Hausa da aka fi sani da sunan Halima 'yar asalin kasar Jamus.

https://p.dw.com/p/2iGW0
DW Taubstumm3
Hoto: Katrin Gänsler

Babayen sun yaba ne a lokacin da marubuciyar da taimakon wasu daga cikin matasansu suke aikin tsara wasu littattafan na alamomin maganar hannu da ma'anoninsu. A bara ne wannan marubuciya Constanze Schmaling da aka fi sani Halima ‘yar Fulani a kasar Hausa ta kaddamar da littafi na uku da na hudu na harshen Bebayen, sannan a bana kuma ta zo da littafi na biyar wanda ta raba wa Bebaye a makarantunsu na yaki da jahilci da ke Kano.

Ta kuma yi alkawarin ci gaba da ba da gudummawa ta musamman.

"Za a ci gaba da irin wannan aiki da muke yi yanzu wato za a kara yin wasu littattafai. An buga guda dubu aka rarraba wa Bebaye kyauta."

Fafutukar da ake yi dai shi ne na ganin cewar Bebayen sun nakalci magana da hannu.