Fada zai yi shekaru 40 a kurkuku a Indiya | Labarai | DW | 02.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada zai yi shekaru 40 a kurkuku a Indiya

Sanil K. James an gabatar da shi a gaban kotu a shekarar 2014 bayan gano fyade ga yarinya da ya yi a wata coci mai suna Salvation Army church wacce ke Kudancin jihar Kerala.

Symbolbild - Proteste gegen Vergewaltigungen in Indien

'Yar fafutkar yaki da cin zarafin mata a Indiya

Wata kotu a kasar Indiya ta yanke hukuncin shekaru 40 a gidan kaso ga wani babban malamin majami'a saboda laifin aikata lalata da wata karamar yarinya ‘yar shekaru 12 kamar yadda mai gabatar da kara ya bayyana a ranar Laraban nan.

Sanil K. James an gabatar da shi a gaban kotu a shekarar 2014 bayan gano wannan aikin cin amana da ya yi a wata coci mai suna Salvation Army church wacce ke a Kudancin jihar Kerala.

Har ila yau wannan fada ana kuma zarginsa da aikata lalata da wata yarinyar baya ga wacce aka gabatar da shi a gaban kotu a kanta a wancan lokaci, kamar yadda Pious Mathew me gabatar da karar ke fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP. A cewar Mathew wannan fada ya dauki tsawon watanni biyu yana lalata da yarinyar wacce ke shekaru 13 a yanzu a cikiin cocinsa.

Kamar yadda hukumar da ke lura da aikata irin wadannan miyagun laifuka a kasar ta Indiya ta bayyana fiye da yara 18,000 ne a ka aikata musu wannan laifi a kasar a shekarar ta 2014, abin da kuma ke faruwa bayan yaran sun aminta da mazambatan.