Fada ya sake barkewa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 16.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada ya sake barkewa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Wani sabon tashin hankali ya barke a gabashin kasar inda fadan da ake yi ya tilasta wa dubban jama'a yin hijira a makobciyar kasar watau Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango.

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya HCR ta ce dubban jama'a sun tsere daga garin Bangassou na Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da ke a yanki kudu maso gabashi kan iyaka da Jamhuriyar Demokaradiyar kwango. Domin gujewa fadan da ya sake barkewa tsakanin Kungiyar Seleka ta Musulmi da ke dauke da makai da kuma Kungiyar Anti Balaka ta Kiristoci a garin na Bangassou. Gwamnatin Kwango ta ce a karshen mako kusan 'yan gudun hijira na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dubu uku ne suka kwararra zuwa garin Bas Uele da ke a arewacin Kwangon, inda cutar Ebola ta sake bula wacce tuni ta kashe mutane guda uku.