Fada ya barke a Somalia | Labarai | DW | 12.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada ya barke a Somalia

Wani mummunan fada ya barke a tsakiyar kasar somaliya ayau,yini guda bayan gwamnatin rikon kwarya na kasar tayi watsi da daftarin sulun da kungiyoyin muslimi suka gabatar mata.Mayakan kungiyoyin musulmin sun cafke garin Bandiradley,bayan sun sanar dacewa mayakan dake marawa gwamnati baya sun afka musu da hari,akarkashin jagorancin dakarun kasar Habasha,a yankin Putland dake kusa da kann iyakokin kasashen biyu.Kakakin kungiyoyin musulmin Mohammad Mahmud Agaweyne,ya fadawa manema labaru ta wayan tarho cewa,har yanzu bangarorin biyu nacigaba da arangasma da juna.Kann shina kakakin rundunar Puntland Sa,id Abdirrahman Dakaweyne,shima ya tabbatar da hakan.Kawo yanzu dai rahotanni na nuni dacewa an kashe mayakan musulmin guda biyu,bugu da kari wasu mazauna kauyyukan guda uku sun gamu da ajalinsu a wannan fada.