Fada ya barke a Bangui | Labarai | DW | 14.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada ya barke a Bangui

An yi wani kazamin fada tsakanin magoya bayan hambararen shugaban Afirka ta Tsakiya Francois Bozize da sojojin 'yan tawayen Seleka a tsakiyar birnin Bangui inda mutane 7 suka kwanta dama.

An yi wani kazamin fada tsakanin magoya bayan tsohon hambararen shugaban kasar Afirka ta Tsakiya da kuma a dai share daya 'yan tawayen da suka kame iko daga kasar.

Fadan ya barke ne a yayin da sojojin 'yan tawayen ke sintiri a tsakiyar birnin na Bangui a unguwar Boy Rabe cibiyar magoya bayan hambararen shugaban inji Janar Nousa Dhaffane kakakin rundunar 'yan tawayen.

A na shi bangare babban jami'in asibitin birnin na Bangui Roman Guetiza ya ce an kai masu gawarwakin mutane kimanin guda bakwai, yayinda aka biya da wasu 9 da suka samu raunika.

A ran Asabar ne komitin koli na 'yan tawayen ya nada jagoran kungiyar ta 'yan tawayen Seleka Michel Djotodia a matsayin sabon shugaban kasar.

Mawallafi: Issoufou mamane

Edita ; Umaru Aliyu